Matsalar Tsaro: Hanya Daya Ce Za'a Bi A Magance Matsalar---Malamin Addini

Matsalar Tsaro: Hanya Daya Ce Za'a Bi A Magance Matsalar---Malamin Addini

 

 

Daga Babangida Bisallah, Minna

 

 

An bayyana sakaci na riko da koyarwa addini da rashin adalcin shugabanni shi ya assasa halin da ake ciki na rashin tsaro a kasar nan. 

Shareef Ishaq Bin Adam, limamin masallacin juma'a na  Tudun Fulani dake garin Minna shi ya bayyana hakan ga wakilinmu bayan kammala sallar juma'a.

Shareef ya cigaba da cewar sakacin al'umma wajen riko da addini yayi tasiri wajen jefa al'umma cikin rashin tausayi da ya kai ga suna kashe yan uwan su da sunan garkuwa dan samun kudin fansa. 
Ya ce wajibi ne shugabanni su dawo daga dogon bacci wajen assasa guiwar al'umma wajen komawa ga tafarkin Allah, sannan su zama adilai.
"Rashin adalci, babban kalubale a tafiyar da shugabancin al'umma domin duk shugaban da ya zama azzalumi, fitintinu za su yawaita a karkashin shi, domin zai zama yana ba da umurni baya tasiri domin maganganunsa ba za su yi tasiri a zukatan al'umma ba. 

"Ina kira ga shugabannin mu da su ji tsoron Allah, su sani akwai ranar da gabobinsu  za su bada shaida akan yadda ya rike amanar da aka damka masa, saboda mashawarta, makusantan shugabanni su taimaka masu wajen lurar da su abubuwan da suka dace ba tunanin yin gulma da tsegumi dan samun abin sanyawa aljihu ba," a kalamansa.
Shareef Ishaq, ya nemi al'ummar kasar nan da su ajiye bambance bambancen da ke tsakanin su na harshe, yanki ko kabila dan hada hannu ta yadda za a tsamo kasar nan daga halin da take ciki yau, idan kana farin ciki akan wani iftila'in da ya samu wani kana ganin ka samu makamin da za ka yake shi lokacin zabe, kafin zaben nan ba ka san irin wadda za ta fada ma ba.

Ya ce matsalar tsaro, tsadar rayuwa abu ne da ya shafi kowa a kasar nan,  wajibi ne mu hada hannu da gwamnati wajen lalubo bakin zaren kafin jirgin ya nutsar da mu baki daya.