Matsalar Man Fetur:Farashin Galan Ya Kai 2000 A Sakkwato

Matsalar Man Fetur:Farashin Galan Ya Kai 2000 A Sakkwato

 

 

Matsalar karancin Man fetur da ake fama da ita a Nijriya, jihar Sakkwato abin ya ta'azara al'ummar sun shiga cikin halin wahala musamman a wurin sufuri anninka kudin da ake daukarsu zuwa unguwannin cikin gari da wajen jiha.

Wasu jama'a sun bayyana cewa karancin man fetur ya saka su a wahala matuka ga shi ba kudi ga rayuwar ta kara kunci.

Bashar Danfari ya ce akwai wahala sosai a wannan karancin man fetur a jihar Sakkwato, "da wannan safiyar ta yau na zagaya ko'ina a cikin gari gidajen Mai a rufe bayan gida biyu dana gani a bude suna sayarwa kan naira 205 a kowace litar mai suma layin man ya fi gaban misali, akwai wanda ko zai samu man sai ya kai marece in har gidan man bai rufe ba, ya ce ya kare," a cewar Danfari
Ya ce anan Sakkwato robar da muke saye naira 80 ta koma 200, wadda muke saye 200 ta koma 400, ta 400 ta koma 700, galan guda 1900 zuwa 2000, a haka ake ta wahalar.
Abubakar Taraliya mai sana'ar tuka babur da ake kira acaba ya ce mai ya yi wahala a wurin 'yan bunburutu ya sayi mansa galan daya kan 1500 kan haka duk in da ake daukar mutum ya biya naira 70 yanzu sai 150 sun ninka ne domin tsadar man.
Yusuf Muhammad ya koka kan yanda matsalar man ke kawo masu matsala ga walwalarsu ya ce ya sayi galan daya kan 2000, sufuri ya yi tsada duk in da za ka je sai ka ninka kudi, ababen hawan ma sun yi karanci a gari.