Matashi Honarabul  Mansur Bello Achida Ya Tallafawa Mata Da Matasa 120 A  Yankinsa

Matashi Honarabul  Mansur Bello Achida Ya Tallafawa Mata Da Matasa 120 A  Yankinsa


Wani matashi Honarabul Mansur Bello Achida , Ya bayyana cewa ya samu hallar mahaifarsa, dake  runfar zabe Kanwuri B  cikin garin Achida domin bada tallafi ga iyayen  mata su dari da ashirin  120  da kuma bada tallafi ga matasan office, tare da Alkawalin dorewa kan hakan.


Ya bayyana cewa an nuna masu So da kauna, inda yayi godiya ga iyayen su mata in da ya bayyana cewa "mu na godiya Allah ya saka muku da mafifincin Alkhairin sa mungode! Mungode"

Honarabul ya fahimci duk wani da a za yi yakamata a sanya mata da matasa gaba don haka ne abin ya dace ga duk mai son cigaba.

Mansur Achida ya nuna kishinsa ga mutanesa kuma zai ɗore da yi masu hidima don samar da al'umma ta gari a yankinsa da jiha baki ɗaya.

Waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun nuna farincikinsu ga wannan karimci da aka yi masu kuma za su yi amfani da tallafin ta hanyar da ya dace.