Matakai Uku Da Za Ku Bi Wajen Maida Tsoffin Naira Banki Duk Da Wa'adi Ya Cika 

Matakai Uku Da Za Ku Bi Wajen Maida Tsoffin Naira Banki Duk Da Wa'adi Ya Cika 

 

 

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a ranar Talata gwamnan babban bankin ya jaddada cewa babu bukatar tsawaita wa'adin tsohon naira a Najeriya. 

Emefiele ya faɗi haka ne duk da umarnin Kotun koli na ci gaba da hada-hada da tsoffin takardun naira har zuwa 15 ga watan Fabrairu, lokacin da zata saurari ƙarar da gwamnoni suka shigar. Legit.ng Hausa ta haɗa maku matakai uku da zaku bi wajen maida tsohon kuɗin ku a rassan CBN da ke jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja. 
1. Cike Fam ɗin CBN Da farko zaku shiga safin yanar gizo-gizo na CBN ku cike Fam daga nan za'a ba ku wasu lambobi ko kuma mutum zai iya zuwa reshen CBN na jiharsa ya karɓi Fam ɗin ya cike. 
2. Katin shaida (I.D Card) Idan zaku je, ku tafi da katin shaidar zama ɗan kasa ko wasu katunan shaida kamar Katin zaɓe. 
3. Za'a baku takardan Tela Na karshe, bayan kun gama cike Fam din, CBN zai baku takardar shaidar cike fam (Teller) kuma zai karbi tsoffin takardun naira da kuke son aje wa domin sa muku a Asusun banki.