Mataiamaki Na Musamman Ga Sanata Wamakko Ya Ajiye Aikinsa

Mataiamaki Na Musamman Ga Sanata Wamakko Ya Ajiye Aikinsa

 

Alhaji Hassan Sahabi Sanyinnawal mataimaki na musamman ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a fannin yada labarai ya ajiye aikinsa.

A takardar da aikowa Managarciya bai  bayyana dalilinsa na ajiye aikin ba.
Sanyinnawal ya ce ya ajiye aikinsa na mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko don haka yana godiya kan damar da ya ba shi ta  yin aiki tare da shi. 
Ya kuma yi godiya ga duk wadanda suka taimaka masa ga samun nasarar aikinsa.