Masu yi wa Tinubu zangon-ƙasa basu da kishin Nijeriya —Bello Matawalle

Masu yi wa Tinubu zangon-ƙasa basu da kishin Nijeriya —Bello Matawalle
Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana wadanda ke shirin kayar da shugaban kasa Bola Tinubu a 2027 a matsayin ’yan siyasa marasa kishin ƙasa.

Ya kuma kara da cewa babu wani taron-dangi da zai hana shugaban kasa tsayawa takara da kuma lashe zaben 2027.

Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan yunkurin da wasu ‘yan siyasar Arewa ke yi na kushe gwamnatin Tinubu, inda su ke bada misali da salon mulkinsa.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ya fitar, ministan ya bayyana kwarin gwiwar cewa masu zaton-ƙasan banza su ci nasara ba, yana mai nuni da irin dimbin alfanun da yankin ke samu a karkashin gwamnatin Tinubu.

Ya ce wadanda ke da karfin mabiya a siyasa na