Masu safarar mutane na samun Dala Biliyan 245 a shekara, in ji gwamnatin taraiya
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa masu safarar mutane na samun ribar dala biliyan 245 a duk shekara, bisa kididdigar Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO).
Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, ya ce daga cikin wannan adadi, dala biliyan 169.9 na fitowa daga cin zarafi ta hanyar lalata, yayin da dala biliyan 75.9 ke fitowa daga aikin tilas, musamman a sashen masu zaman kansu ciki har da aikin gida.
Fagbemi ya bayyana haka ne a Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki karo na 28 domin bikin ranar yaki da safarar mutane ta duniya. Ya ce safarar mutane laifi ne mai tsari wanda ke barazana ga tsaron kasa, kasancewar Najeriya na matsayin asali, hanya da makoma ga masu safarar mutane.
Ya bayyana cewa hukumar NAPTIP ta ceto mutane 25,642, ta kama wadanda ake zargi 11,406, tare da samun hukunci 750 tun kafuwarta.
A nata jawabi, Darakta Janar ta NAPTIP, Binta Bello, ta ce masu safara na amfani da dabaru iri-iri kamar tayin bashi ta yanar gizo da karatu na bogi don jefa mata cikin cin zarafin ta hanyar lalata da aikin tilas.
Ta kuma bayyana cewa ana daukar matakai na hadin gwiwa da sauran kasashe domin tabbatar da dawo da wadanda aka safar da su cikin aminci tare da hukunta masu laifi.
A nasa bangaren, wakilin UNODC a Najeriya, Cheikh Toure, ya bukaci gina tsarin kasa na tattara bayanai a kan safarar mutane domin samun sahihiyar dabarar yaki da wannan laifi mai hatsari.
managarciya