Malam Tukur Mamu Na Hannun Daman Shaikh Gummi Na Hannun DSS
Hukumar ƴan sandan farin kaya, DSS, ta ce Tukur Mamu, wanda ke sansanci da ƴan ta'adda da su kai garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, ya na hannunta.
A yau Laraba ne dai rahotanni su ka nuna cewa jami'an tsaro sun kama Mamu ɗin a filin jirgin sama na Cairo, ƙasar Egypt a kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya da iyalansa.
Sai dai kuma a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na DSS, Peter Afunanya ya fitar a yau Laraba a Abuja, hukumar ta tabbatar da cewa ya na hannunta bayan an dawo da shi daga Egypt.
Sanarwar ta ce an kama Mamu ne bisa umarnin hukumomin soji da na tsaro da kuma na tsaron sirri domin ya amsa wasu muhimman tambayoyi a kan binciken da ake yi kan yanayin tsaro a wani ɓangare na ƙasar nan.
managarciya