Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya kalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta yi wa ‘yan Najeriya bayani kan yadda aka tafiyar da kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.
Atiku ya ce akwai buƙatar gwamnati ta yi cikakken bayani kan kusan Naira tiriliyan 30 da ya ce aka samu sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da kuma cire tallafin mai.
Ya bayyana cewa kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur na ‘yan Najeriya ne, don haka ya kamata gwamnati ta fito fili ta bayyana yadda aka kashe su da kuma irin ayyukan da aka gudanar da su.
Atiku ya kuma tambayi gwamnatin Tinubu dalilin da ya sa har yanzu ba a samu cikakken bayani kan inda kuɗaɗen suka dosa ba, yana mai jaddada cewa ‘yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda ake amfani da kuɗaɗen ƙasar.
Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta yi cikakken bayani kan makomar kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin mai.






