Home Rahoto Majalisar waƙillai ta zauna da hukumar aikin Hajji domin kaucewa matsalolin da...

Majalisar waƙillai ta zauna da hukumar aikin Hajji domin kaucewa matsalolin da ke samu a Saudiyya

18
0

Kwamitin Addini na Majalisar Wakilai ya gana da Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa NAHCON kan shirye-shiryen Aikin Hajji da kuma matsalolin da mahajjatan Najeriya ke fuskanta.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Kwamitin, Muhammad Nalaraba Chiroma, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Shu’aibu Ado, ya fitar.

Sanarwar ta ce an tattauna batun matsalolin biza da hanyoyin samar da ingantaccen tsarin kula da mahajjata tun daga gida Najeriya har zuwa ƙasa mai tsarki.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an kuma tattauna hanyoyin inganta kula da lafiya da tsaron mahajjata yayin gudanar da Aikin Hajji.

Mataimakin Shugaban Kwamitin, Muhammad Nalaraba Chiroma, wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Gezawa da Gabasawa na Jihar Kano a Majalisar Wakilai, ya bayyana buƙatar samar da gyare-gyare domin inganta shirye-shiryen Aikin Hajjin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here