Majalisar Dokokin Zamfara Ta Fadi Dalilin Da Ya Sanya Ta Tsige Shugabanta

Majalisar Dokokin Zamfara Ta Fadi Dalilin Da Ya Sanya Ta Tsige Shugabanta

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, sannan ta nada Bashar Gummi a matsayin kakakin majalisa na wucin gadi.

Hakan ya biyo bayan kudirin da 'dan majalisa mai wakiltar mazabar Maru, Nasiru Abdullahi ya gabatar, inda mambobi 18 cikin 24 suka amince da shi. 

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, mambobin majalisar 18 daga cikin 24 sun amince da tsige kakakin yayin wani taron gaggawa da suka gudanar a daren Alhamis, 22 ga watan Fabrairu. 

A cewar mambobin majalisar, an dakatar da kakakin majalisar ne saboda matsalar tsaro da ke addabar jihar da tare da majalisar ta yi wani yunkuri na dakatar da annobar ba.
'Yan majalisar sun bukaci a sabon kakakin majalisar da aka nada da ya yi amfani da matsayinsa wajen kawo karshen ‘yan bindiga da suka kusan gurgunta tattalin arziki a jihar. 
Daya daga cikin 'yan majalisar, Shamsudeen Basko, mai wakiltar mazabar Talata Mafara, ya yi jan hankali ga sabon kakakin majalisar.
Basko ya bayyana cewa batun rashin tsaro na daya daga cikin muhimman batutuwan da ya kamata a bai wa fifiko wanda ya sa aka dakatar da tsohon kakakin, rahoton Blueprint.
Basco ya ce “Ina da batutuwa guda biyu, amma an yi nazari a kan daya, wato na rashin tsaro da ke damun jama’armu. A kullum ana kashe mutanenmu ana garkuwa da su.