Majalisar Dokokin Sakkwato Ta Sanya Tambuwal Gaba Kan Sai Ya Gudanar Da  Wasu Aiyukka a Kananan Hukumomi Biyu

Majalisar Dokokin Sakkwato Ta Sanya Tambuwal Gaba Kan Sai Ya Gudanar Da  Wasu Aiyukka a Kananan Hukumomi Biyu

 

Majasalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta aminta da kudirin doka wanda 'yan  majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Gada ta Gabas Honarabul Kabiru Dauda dana Goronyo Faruku Amadu  suka gabatar kan neman gwamnatin jihar Sakkwato ta gyara hanya mai tsawon kilomita 35 daga garin Gada ta hada wasu kauyukka har zuwa gulbin Bakalori a cikin Gada da Goronyo. Honarabul Alhaji Maidawa ya goyi bayan kudirin. 

A karshe dai majalisa ta aminta da ta yi kira ga gwamnatin jihar Sakkwato da ta gyara hanyar wadda ta taso daga garin Gada ta hada da kauyukkan Ilah Gari, Tsuga, Dogon dajin faru, Dukamaje, Gidan Kuka, Rumbukawa, Gilbadi, Sabon gari, Darnawa, Manmansuka, Sakitawa, duk a kananan hukumomin Gada da Goronyo.

Haka ma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Illela Bello Isah Ambarura ya sanar da wani aikin gaggawa da ake bukatar gwamnatin jiha ta aiwatar waton gyara Gadar Dogon Karfe-Sandaga kan hanyar Sakkwato zuwa Illela.

Majalisa ta aminta da kiran hukumomin da lamarin ya shafa gwamnatin Sakkwato da karamar hukumar Illela su yi wani abu na gyara Gadar da ta karye.

 

Haka ma ta yi kira da hukumar kula da gyaran  hanyoyin gwamnatin tarayya FERMA da su yi wani abu don gyara Gadar.

Abin jira a gani wannan kiran da matsayar da majalisa ta cimma za ta bibiyi lamarin har ta tabbatar da an aiwatar da shi ko kuma waka ce kawai aka rerawa Sakkwatawa don su raya komi ya wuce busar mabushi a gidan Sarki.