Majalisar Dokokin Bauchi Ta Amince Da Amfani Da Harshen  Hausa Wurin Aiwatar Da Ayyukanta

Majalisar Dokokin Bauchi Ta Amince Da Amfani Da Harshen  Hausa Wurin Aiwatar Da Ayyukanta

Majalisar Dokokin Bauchi Ta Amince Da Amfani Da Harshen  Hausa Wurin Aiwatar Da Ayyukanta

 
Majalisar dokokin jihar Bauchi, ta sanya harshen Hausa baya ga turanci cikin yarukan gudanar da harkokinta. Kakakin majalisar, Honarabul Abubakar Y Suleiman ne ya sanar da hakan a zauren majalisar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Shira, Honarabul Auwal Hassan ne ya gabatar da wannan ƙudirin a ranar Talata. 
Da yake gabatar da ƙudirin, Hassan ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar da cewa za a riƙa gudanar da abubuwan gwamnati da ma waɗanda ba na gwamnati ba cikin harshen Turanci. 
Sai dai ya ce wata doka da majalisar jihar ta yi a shekarar 2017, ta bai wa majalisar ikon gudanar da harkokinta cikin harshen Turanci ko wani ɗaya daga cikin yarukan da ake da su a jihar. Ya ƙara da cewa, harshen Hausa ne sama da kashi 90% na al’ummar jihar Bauchi ke amfani da shi wajen sadarwa, wanda da hakan ne ya ba da shawarar a ƙara da shi baya ga Turanci a matsayin yare na biyu da za a riƙa amfani da shi. 
Da yake nuna bayansa, Honarabul Musa Wakili Nakwada, wanda ke wakiltar mazaɓar Bogoro, ya yabawa abokin aikinsa kan ƙudirin, inda ya bayyana cewa ya taɓa gabatar da ƙudirin a majalisa ta 9 da ta shuɗe. A yayin da kakakin majalisar ya gabatar da ƙudirin domin jin ra'ayoyin sauran jama'a, sun amince da shi ba tare da wani tarnaƙi ba.