Home Rahoto Majalisar dattawa ta kafa kwamitin jin ra’ayoyin ‘yan majalisar game da dokar...

Majalisar dattawa ta kafa kwamitin jin ra’ayoyin ‘yan majalisar game da dokar zaɓe

11
0

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da kafa wani kwamiti domin tattara ra’ayoyin sanatoci kan dokar zaɓe.

Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan zaman sirri da majalisar dattawa ta yi, inda ‘yan majalisar suka tattauna rahoton kudirin dokar.

Ya ce, “Majalisar Dattawa ta kafa ƙaramin kwamiti domin ƙara ba da gudunmawa, tattarawa da tace dukkan ra’ayoyin sanatoci, sannan a gabatar mana da su domin tattaunawar ƙarshe a ranar Talata.”

Akpabio ya ce an zaɓi Niyi Adegbomire, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin shari’a da doka, a matsayin shugaban kwamitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here