Mahara Sun Kashe Dan Kwamishinan Tsaro A Harin Da Suka Kai Zamfara

Mahara Sun Kashe Dan Kwamishinan Tsaro A Harin Da Suka Kai Zamfara
 
 
Mahara Sun Kashe Dan Kwamishinan Tsaro A Harin Da Suka Kai Zamfara
 
Wasu 'yan bindiga ranar Lahadi da daddare, sun kai hari garin Tsafe. hedkwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, sun halaka mutane da dama. 
 
Mazauna garin sun bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗan da aka kashe shi ne ɗan Kwamishinan harkokin tsaro na jihar Mamman Tsafe. 
 
Sai dai har yanzun, kwamishinan da kuma gwanatin Zamfara ba su ce uffan dan tabbatar da lamarin a hukumance ba. 
 
Haka nan, kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, bai ɗaga kiran wayan da Premium Times ta yi  masa ba, kuma be turo amsar sakon da aka tura masa  ba. 
 
Mazauna garin sun bayyana cewa 'yan bindigan sun shigo garin jim kaɗan da gama Sallan Tarawihi, suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi. 
 
Bayanai sun nuna cewa 'yan ta'addan sun halaka aƙalla mutum uku, kuma lamarin ya auku a yankin Hayin Tumbi kusa da gidan Kwamishinan. 
Jihar Zamfara na cikin wuraren da 'yan bindiga ke cin karensu ba babbaka waton suna yin yanda suka dama da rayuwa da dukiyar jama'a.