Mahaifan Fatima Da Ta Rasa Kafarta Sun San Da Wannnan?

Mahaifan Fatima Da Ta Rasa Kafarta Sun San Da Wannnan?

 

Sama da wata daya kenan al'amari na ban tausayi da kada zuciya ya samu daliba Fatima, a ranar da ta kammala jarabawar karshe ta Sikandare in da wani matashi Aliyu ya buge ta da mota abin da ya yi sanadin ta rasa kafarta har abada, domin an yake ta ganin ba ta gyaruwa.

Karancin shekarun yarinyar da yanda aka ta yada lamarin ya karkato hankalin mutane masu tausayi da nema mata hakkinta ganin kamar ba za a yi mata adalci ba.
Managarciya na cikin kafafen yada labarai da suka fara yada labarin wannan matashiya, in da suka yi fira da ita a kan gadon asibiti a UDUTH dake Sakkwato don ganin an yi mata adalci.
Wannan gwagwarmayar ta sanya mahaifan Fatima sun kawar da kansu kan abubuwa da yawa da muke ganin yakamata a tunatar da su, domin duk mutu dan Tara ne bai cika 10 ba.
Mahaifan Fatima bai kamata su manta da karimci da mutuntawar da mahaifan Aliyu da kaddara ta sanya ya zama silar raba ta da kafarta suka yi ba, "a lokacin  da Aliyu ya take kafar Fatima  ya sanar da mu, ba wani bata lokaci muka tafi makaratar da abin ya faru muka samu an tafi asibiti, a haka muka je har aka kammala yi mata aiki, duk wata dawainiya da mu aka yi ta, tare da bayar da kudi, na zubar da hawaye kan tausaya wa ganin wannan yarinya ta rasa kafarta  a sanadiyar dana, na bayar da hakuri ban san adadi ba a kasa na durkusa gaban mahaihiyar Fatima domin nasan wannan lamarin da ciwo yake matuka.

"Mun  sanar da su ko sirinji za a saya mun dauki nauyin jinyar Fatima gaba daya, bayan ta warke za mu yi mata kafar roba, fatar mu su karbi wannan kaddarar da muka zama sila, mun yi ta kokarin samun silhu kan lamarin abin da bai samu ba, duk da shigowar hukumar kula hakkin dan Adam da mai baiwa gwamna shawara kan kungiyoyi masu zaman kansu Hajiya Ubaida Bello, abin ya ci tura," kalaman mahaifiyar Aliyu Kenan.
Mahaifan Fatima shin sun san samun nasara kan mahaifan Aliyu da suke nema don ganin sun fi su gaskiya ba zai sanya kafar Fatima ta dawo ba, kuma ba zai taba wanke tabon bacin ran da suka shiga ba, hasalima rama kyakkyawa ga wanda ya yi maka sharri shi ne zai taimaki sauran rayuwar Fatima a kalubalen rayuwa dake samun mutane lokaci bayan lokaci.
Mahaifan Fatima sun fahimci wa'zain da Allah ya yi masu abin da suka ki karba a wurin iyayen Aliyu cikin rufin asiri  shi ne suka karbaa wurin wasu attajirai a Abuja.
Shin sun san wannan abin da ya same ta ba wanda ya isa ya hana samuwarsa domin kaddara ce ta Allah, amincewa da ita da yarda da yin silhu kadai ne zai sa Allah ya yi riko da hannun Fatima a cikin wannan jarabawar da ta samu.

Shin mahaifan Fatima sun san yanda ba za su iya hana hakan ya same ta ba, hakan ba za su iya tsara yanda rayuwarta za ta kasance a gaba ba, don tunanin a tara mata kudin diya da sanya bacin rai a mahaifan Aliyu, rungumar yafiya da hakuri ne kadai makamin da zai taimaki rayuwar Fatima a cikin jarabtar da ta samu ta har abada.
Shin mahaifan Fatima sun san Aliyu mutumin kirki ne a rayuwarsa ya hadu da wannan kaddarar da ya zama silar sanya bakin ciki ga Fatima, su sani zama gidan yari bana masu hali irin na Aliyu ba ne, kar babban hakki na 'yar su ya sa su manta da karamin hakkin Aliyu da dokar kasa da addininsa ya ba shi.