Magoya Bayan PDP Lokaci Ya Yi Da Za Su Jingine Adawa Domin Ciyar Da Sakkwato Gaba---Aminu Ganda

Injiniya Aminu a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala yanke hukuncin kotun koli da ta tabbatar da nasarar APC da Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ya ce lokaci ne na gina Sakkwato don ta samu cigaba.

Magoya Bayan PDP Lokaci Ya Yi Da Za Su Jingine Adawa Domin Ciyar Da Sakkwato Gaba---Aminu Ganda

Jigo a jam’iyar APC a jihar Sakkwato Injiniya Aminu Ganda ya yi kira ga jam’iyar adawa a Sakkwato ta jingine adawa domin ciyar da jiha gaba.

Injiniya Aminu a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala yanke hukuncin kotun koli da ta tabbatar da nasarar APC da Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ya ce lokaci ne na gina Sakkwato don ta samu cigaba.

“Gaskiya ta yi halinta,  jayayyar da PDP ke yi lamari ne kawai na tafiya kotu amma wadanda ke jefa kuri’a an san APC  suka zaba a jihar Sakkwato  zuwan da suka yi ba illa ba ne, yanzu tunda kotu ta tabbatar da zabin jama’a muna fatar su zo a hada kai su taimaka a ciyar da Sakkwato gaba kamar yadda Gwamna ya fara, muna fatar za su ajiye adawa su zo  don a ciyar da Sakkwato gaba shi ne fatana.”

Ya kake ganin za a jingine adawa bayan ita ce gishinrin dimukuradiyya? ya ce “yauwa ai duk adawar da take ta son cigaba mai kyau ce, ina nufin su jingine adawa anan su rika amfani da basirar su in mai girma gwamna ya yi abin cigaba  su yaba, ba kushewa za su yi ba, kuma su kusanci gwamna domin bashi shawara ta gari. A Sakkwato a gashi nan ana aiyukka na cigaba wanda a baya an barsu a yabi gwamna da wannan ita ce adawar kwarai,” a cewar Injiniya Ganda.

Ya juya kan zaton  da wasu ‘yan adawa ke yi na za a yi masu bita-da kulli ya ce “tun sanda Ahmad Aliyu yake yekuwar zabe ya fadi duk abin da zai kawowa Sakkwato cigaba shi zai yi kuma mu da ke tare da shi muna da yakinin mutum ne mai adalci da son kimanta gaskiya a mulki, tun sanda aka fara gwamnati ba a musgunawa ‘yan adawa ba, a yanzu ma ba za a yi masu ba, su ne suka saba cin zarafin mutane shi ne suke tunanin za a yi masu su kwantar da hankalinsu hakan ba zai faru ba.”