Magoya Bayan Abdul'aziz Yari Sun Zargi Buhari Ya Yi Masu Butulci

Magoya Bayan Abdul'aziz Yari Sun Zargi Buhari Ya Yi Masu Butulci

 

Magoya Bayan tsohon gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da yi masu butulci a lokacin da yakamata ya mayar da buki kan abin da suka yi masa a baya.

Alhaji Mustafa Abubakar Yari ya ce a yanzu sun gane shugaban kasa Buhari bai yi masu adalci ba, "Yakamata shugaban kasa ya tuna yanda Abdul'aziz Yari ya yi tallarsa, ya manta sanda ya yi rantsuwa cewa da gwamnonin Nijeriya irin Abdul'aziz ne ba zai  yi takara ba, ya kamata shugaban kasa ya rika biyar doka.

"Shugaban kasa bai kyautawa Abdul'aziz ba, ni kaina sau sha uku ina tafiya Saudiya ina rokon Allah da hawayena ka zama shugaban kasa, Allah ya karbi addu'a shi ne ka sakawa Zamfarawa da haka," a cewar Mustafa Yari.
A bayanin da ke fitowa a wurin babban taron APC na kasa jagororin jam'iya sun tabbatar da sauran masu takarar shugaban jam'iyya na kasa sun jaye an bar wanda Buhari ke so waton tsohonn gwamnan Nasarawa Abdullahi Adamu abin da bai yi magoya bayan Abdul'aziz Yari dadi ba.
Magoya bayan Yari sun yi ta kalamai munana na fushi ga shugaban kasa saboda suna ganin ba a yi masu adalci ba.

Wasu bayanai da ba a tabbatar ba da MANAGARCIYA   ta samu sun ce tsohon gwamnan ya yi fushi da wannan matakin da jagororin APC suka dauka na kange shi ya shiga cikin takarar shugabancin jam'iyyar wadda yana cikin masu hannu da kafa ta da yi mata riga da wando har zuwa samun nasararta.
Haka ma ana hasashen wannan hasalar da ya yi zai bar jam'iyar ne gaba daya nan da wasu kwanaki masu zuwa.
Yari ya bayar da sanarwar janye takararsa ta shugabancin jam'iyyar amma ba zai halarci taron gangamin ba, kamar yadda wata majiya ta sanar.

A kwanan baya tsohon gwamnan ya yi zama da wasu jagororin PDP abin da ya karya ta haduwar ba ta da nasaba da barin APC, amma a yanzu kan halin da ake ciki ana ganin Shehi lokaci ne kawai yake jira ya bar APC.
Duk yunkurin jin ta bakin makusantan gwamnan kan lamafrin bai samu ba.