Maganin Ciwo 7 Da Tafarnuwa Ke Yi Bayan Amfani Da Take Da Shi A Lafiyar Jiki

Maganin Ciwo 7 Da Tafarnuwa Ke Yi Bayan Amfani Da Take Da Shi A Lafiyar Jiki
Man Tafarnuwa

SIRRIN MU MATA GROUP


AMFANIN MAN TAFARNUWA 

Tafarnuwa tana daga cikin Tsirrai mafi amfani waɗanda Duniya ta daɗe tana amfana da su. Annabi (S.A.W) ya tabbatar da cewa tana da amfani sai dai ba ya cinta saboda dalilin warin da take da shi. 

Wata rana an ba shi kyautar wani abinci wanda aka hada da tafarnuwa, sai bai ci ba. Ya aika da shi zuwa wajen Abu Ayyub Al-Ansariy (R.A). Sai Abu Ayyub ya ce "Ya Rasulallahi kai baka son shi amma ka aiko min?. 
Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "NI INA GANAWA DA WANDA KAI BAKA GANAWA DA SHI". (Wanda yana ganawa da Mala'ika Jibreelu, su kuma Mala'iku ba su son duk wani abu mai wari). 
Ga wasu kaɗan daga fa'idodin da take ɗauke da su kamar yadda bincike na masana ya tabbatar:


1. CIWON DAJI (CANCER) : Duk mutumin da yake fama da ciwon daji ya yawaita amfani da tafarnuwa. In sha Allahu zai samu waraka. Idan ciwon Cancer din akan fatar jikinsa ne, sai ya rika shafawa ajikinsa bayan yasha cokali guda tare da zuma. Idan kuma Sanƙaran mama ne (Breast Cancer) wanda Mata suke fama da shi, to duk matar da take fama da wannan ciwon ta rika yawan yin girki da tafarnuwa (kamar Jollof rice, ko Pepper Soup, da sauransu). Sannan ta riƙa shan tafarnuwar wacce aka gauraya tare da Man habbah, kuma tana shafawa ajikin Maman. In sha Allahu za ta warke.


2. BASUR : Duk wanda basur yake damunsa, ko yana shan wahala wajen fitar bayan gida, ko kuma masu yin bayan gida da jini, ko masu fama da Kumburin ciki, ko ƙaiƙayin dubura, Ga wani albishir gare ku: Ka je ka samo tafarnuwarka mai kyau. (kamar guda biyu ko uku manya) Ka cire bawon sannan ka bayar a daka maka Fura da ita. Ka samu nono mai kyau kasha wannan furar da shi. In sha Allahu awannan ranar ko washe gari duk za ka fitar da basur ɗin dake cikinka. Kuma za ka samu lafiya da izinin Allah. Sannan ka riƙa gauraya Man Tafarnuwar tare da zuma kana sha kullum da safe. In sha Allahu kai da basur kunyi sallama.

3. SANYI KO KUMBURIN JIKI : Duk mutumin da sanyi ya kumbura shi, ko kuma sanyin ya ratsa shi, kullum hancinsa ba ya rabuwa da majina, shima ga albishir : Ka samo Ganyen Na'a-Na'a ka dafa tare da citta. Sannan ka zuba Man tafarnuwa cokali guda a ciki. Ka sanya zuma sannan kasha. Haka zaka riƙa yi har sati guda zuwa kwanaki 10. Kuma kana shafa man tafarnuwar ajikinka In Allah ya yarda jikinka zai sabe, sanyin zai fita, kuma zaka warke.

4. SANYIN QASHI RHEUMATISM) : Masu fama da sanyin Qashi ko kuma Rikewar gabobi (Arthritis) ga naku : Ku samo Man tafarnuwa mai kyau, ku gauraya shi da Man Habbatus sauda, Sannaan a ɗora shi bisa wuta mai ci a hanakali. Idan ya yi kamar minti biyar sai a sauke. Wannan man mai ɗumi za'a riƙa shafawa ajikin Qafar, ko bayan, ko kwankwaso, ko Qafar da take ciwon. In sha Allahu ko da ciwon bayan yafi shekara goma ana fama, to za'a samu lafiya da izinin Allah.


5. HAWAN JINI DA CIWON ZUCIYA: Bincike ya tabbatar da cewa tafarnuwa tana narkar da mummunan kitsen nan na Cholesterol wanda shi ne yake toshe Kofofin zuciyar ɗan Adam, har ake samun hawan jini ko ciwon zuciya. To tafarnuwa tana narkar dashi kuma tana bude duk hanyoyin da suka toshe din. Sannan tana tsaftace jinin jikin Dan Adam. Ana so masu fama da hawan jini suyi wannan hadin domin samun kuzari da lafiya : A samo ganyen Zogale danye adafashi tare da tafarnuwa. Bayan an taceshi kafin asha sai a sanya Man Zaitun cokali guda, asanya zuma sannan asha. Kuma ayawaita cinta acikin abinci yau da kullum. In sha za'a dace.

6. TYPHOID FEVER (ZAZZABIN HANJI) DA KUMA ULCER : Duk masu fama da wannan larurar ga magani nan da yardar Allah : Ka rika shan cokali guda na tafarnuwa gauraye da zuma kullum da safe, minti 30 kafin breakfast. In sha Allahu wannan zai kashe duk kwayoyin chutar dake cikin cikinka. Hakanan masu macijin ciki ko Tsutsar ciki su ma tsotsotsin zasu mutu. Kuma zasu fita da izinin Allah. Hakanan masu fama da gyambon ciki (Ulcer) su ma zasu samu saukinta idan suka bi wannan hanyar. Kuma su rika sanya cokali guda dlna man tafarnuwar acikin dukkan abincin da zasu ci. Ko kuma arika dafa abincin tare da ita.

7. CIWON HANTA: Tafarnuwa tana bama hantar 'Dan Adam kariya daga chutattuka. Kuma amfani da ita yana hana kitsen nan na cholesterol taruwa ko ginuwa ajikin hanta, ballantana har a samu matsalar ciwon ciki ko Kumburin Hanta. Masu ciwon hanta su rika shan man tafarnuwa ko garinta wanda aka cakuɗa da zuma. 
In sha Allahu za'a ga abun mamaki wato samun lafiya cikin ƙanƙanin lokaci. 

MRS Basakkwace.