Mace za ta iya zama shugabar karamar hukuma a Zamfara----Uwargidan Gwamnan Zamfara

Mace za ta iya zama shugabar karamar hukuma a Zamfara----Uwargidan Gwamnan Zamfara

 

 

Matar Gwaman jihar Zamfara Hajiya Huriya Dauda Lawal ta bayyana zimmar da take da ita na ganin a zabe na gaba mace ta zama shugabar karamar hukuma a jihar Zamfara.

A hirarta da manema labarai a Gusau jihar Zamfara Hajiya Huriya ta ce zaben mata Kansiloli 14 da aka yi babban cigaba ne da mata suka samu a haujin dimukuradiyya a jihar.
Uwargidan Gwamnan ta nuna bukatar da ake da ita ga shugabannin kananan hukkumomi da su baiwa kansiloli goyon baya domin sauke nauyin da aka daura masu .
"Za mu tabbatar da mata kansiloli a jiha an ba su dama iri daya da ta kwarorinsu maza a wurin gudanar da aiyukkan cigaban al'umma."
Matar gwamna ta ce Mata a matsayinsu na uwaye suna da rawar da za su taka wurin samar da romon dimukuradiyya, musamman a fannin kiyon lafiya da makamantansu.
Huriya Dauda ta yabawa jam'iyar PDP a jiha kan wannan damar da ta baiwa mata suka yi takara a zaben kananan hukumomi da ya gabata, "yawaita fitowar mata neman takarar ne ya sanya aka samu yawan mata a kujerun kansiloli a Zamfara."
Ta yi kira da a samar da wayewar kai ga mata a harkokin siysa don a magance mamayar da ake yi masu a harkokin yau da kullum.