Home Siyasa Littafi Ya Gano Yadda Aka Yi Amfani Da Obi Don Daƙile Nasarar...

Littafi Ya Gano Yadda Aka Yi Amfani Da Obi Don Daƙile Nasarar Atiku a 2023

35
0

An samu sababbin bayanai kan yadda tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, da abokan siyasarsa suka yaki jam’iyyarsu a 2023. ‘Yan G5 a PDP sun yi aiki da Bola Tinubu domin kassara Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa da ‘dan takaransu na jam’iyyar PDP ya zo na biyu.

An samu sababbin bayanai kan yadda tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, da abokan siyasarsa suka yaki jam’iyyarsu a 2023. 

‘Yan G5 a PDP sun yi aiki da Bola Tinubu domin kassara Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa da ‘dan takaransu na jam’iyyar PDP ya zo na biyu.

‘Yan adawar sun yaƙi jam’iyyar PDP a wasu jihohin da ake ganin Atiku Abubakar yana da ƙarfi saboda kawai a gyara wa Bola Tinubu hanyar nasara. 

Simon Kolawole wanda marubuci ne ya shaida haka a littafin da ya rubuta: Winning Formula: The Inside Story of Nigeria’s 2023 Presidential Election. 

An tsara cewa za a fara sayar da littafin ga jama’a a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba 2026. A cewar littafin, Wike da abokansa a PDP sun haɗa kai da wasu gwamnonin jam’iyyar APC domin tsara dabarar zaɓe da za ta raunana Wazirin Adamawa. 

Dabarar ta ƙunshi taiimakon Peter Obi a jihohin da PDP ke da ƙarfi, musamman inda ake ganin takarar Musulmi da Musulmi ba za ta kai labari ba.

Abin mamaki shi ne, Obi bai cikin wannan lissafi, kuma mai yiwuwa bai san cewa ana amfani da farin jininsa, an yi wasa da hankali da masoyansa ba. 

A cewar Kolawole, dabarar ta samo asali ne bayan Atiku ya doke Nyesom Wike a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP da aka yi a watan Mayun 2022. 

 ‘Yan siyasar sun yi wasu ganawar sirri a biranen London da Paris saboda APC ta yi galaba a 2023.

 Littafi ya tona dabarar da G5 suka yi Simon Kolawole wanda marubuci ne ya shaida haka a littafin da ya rubuta: Winning Formula: The Inside Story of Nigeria’s 2023 Presidential Election. An tsara cewa za a fara sayar da littafin ga jama’a a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba 2026. 

A cewar littafin, Wike da abokansa a PDP sun haɗa kai da wasu gwamnonin jam’iyyar APC domin tsara dabarar zaɓe da za ta raunana Wazirin Adamawa. Dabarar ta ƙunshi taiimakon Peter Obi a jihohin da PDP ke da ƙarfi, musamman inda ake ganin takarar Musulmi da Musulmi ba za ta kai labari ba.

Abin da ‘yan Arewa suka gujewa da ya hana Tinubu faduwa a zaben 2027’ Abin mamaki shi ne, Obi bai cikin wannan lissafi, kuma mai yiwuwa bai san cewa ana amfani da farin jininsa, an yi wasa da hankali da masoyansa ba. Ganawar sirrin ‘Yan G5 a London da Paris A cewar Kolawole, dabarar ta samo asali ne bayan Atiku ya doke Nyesom Wike a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP da aka yi a watan Mayun 2022. 

Sannan aka yi watsi da shi, aka zaɓi Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin abokin gami. 

Shawarar da su Atiku suka dauka shi ya fara jawo rashin jituwa tsakaninsa da ɓangaren Wike, kuma wannan ya taimaki Tinubu da jam’iyyarsa ta APC. 

Mutanen Wike sun kunshi Gwamnonin jihohi – Samuel Ortom na Benue, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu. A ɓangaren Tinubu kuma, akwai gwamnonin APC: Atiku Bagudu na Kebbi, Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa da Babajide Sanwo-Olu na Legas. Marubucin ya ce na karshensu shi ne Kayode Fayemi wanda ya taba yin gwamna a jihar Ekiti. 

Bayan nazarin manyan ‘yan takarar, sun fahimci Atiku ne babban abokin hamayyar Tinubu a zaɓen. 

Duk da cewa Obi yana samun karɓuwa sosai a tsakanin matasan kudancin Najeriya, sun lura cewa ba zai iya zama shugaban Najeriya a ƙarƙashin LP ba. 

Don gana suka shiga shirya yadda za a lalata ƙuri’un PDP ta hanyar ƙarfafa mutane su zaɓi Obi a yankunan da Atiku yake sa ran samun nasara da kyau.

Lissafin da suka yi shi ne, ƙuri’un da Obi zai samu maimakon Atiku za su amfani Tinubu a ƙarshe, ko da kuwa jam’iyyarsa ba ta lashe waɗannan jihohin ba. 

Lissafin da suka yi shi ne, ƙuri’un da Obi zai samu maimakon Atiku za su amfani Tinubu a ƙarshe, ko da kuwa jam’iyyarsa ba ta lashe waɗannan jihohin ba.

A cewar Kolawole, abin da mutane da dama suka ɗauka a matsayin rashin fayyace matsayar Ortom kafin zaɓen, a zahiri wani ɓangare ne na dabarar siyasar. Da sakamako ya fito kuwa Obi ya samu ƙuri’u 308,372 a Benue, inda ya zo na biyu bayan Tinubu, sai shi Atiku da ya yi takara a PDP ya samu ƙuri’u 130,081. Idan aka kwatanta da zaɓen shugaban ƙasa na 2019, Atiku ya samu ƙuri’u 356,817 ne a jihar Benue.

Littafin ya ce haka su Wike suka yi a jihar Plateau a 2023, wadda ita ma take da yawan Kiristoci. Dama an gaya masu tikitin Musulmi da Musulmi ba zai karbu a Pleateau ba. A madadin haka sai suka taimaki LP don hana Atiku samun ƙuri’un da yake so. 

Atiku, wanda ya samu ƙuri’u 548,665 a 2019, ya tashi da 243,808 kacal a 2023 shi kuwa Obi ya ci jihar da ƙuri’u 466,272, APC mai ƙuri’u 307,195 ce ta biyu. 

Kolawole ya ƙara nuna an yi irin wannan dabara jihohin Edo, Delta da Cross River, inda ake zargin Wike ya yi amfani da tasirinsa wajen kawo cikas ga Atiku. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here