Lamari Ya Canza, Jami’ar Amurka Ta Yi Karin Haske Dangane da Takardar Shaidar Tinubu

Lamari Ya Canza, Jami’ar Amurka Ta Yi Karin Haske Dangane da Takardar Shaidar Tinubu

Lamari Ya Canza, Jami’ar Amurka Ta Yi Karin Haske Dangane da Takardar Shaidar Tinubu 

 
Jami’ar CSU da ke kasar Amurka ta ce ba ta dauke da irin takardar shaidar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatarwa INEC. Caleb Westberg wanda shi ne Magatakardar jami’ar ya shaida haka da yake amsa tambayoyi, Daily Trust ta fitar da rahoton a ranar Laraba. 
Kamar yadda Lauyoyin Atiku Abubakar su ka bukata a kotu, an kira jami’in jami’ar ya amsa wasu tambayoyi da za su taimakawa binciken. 
 
Ana sa ran ‘dan takaran shugaban kasa na PDP a zaben 2023, zai yi amfani da bayanan a kotun koli inda yake kalubalantar Tinubu. 
Atiku ya na ikirarin akwai sabani tsakanin takardar shaidar kammala jami’ar da Tinubu ya gabatarwa INEC da asalin na makarantar. Yayin da yake amsa tambayoyi, Westberg ya ce ba zai iya magana kan takardar da Tinubu ya mikawa INEC ba domin bai taba ganin ta ba. "Jami'a ta na rike da takardar shaidar da dalibai ba su karba ba ne kurum. Jami’a ba ta ajiye satifiket. 
"Ba mu dauke da takardar shaidar da (Bola Ahmed Tinubu) ya gabatarwa Hukumar INEC a hannunmu.
Da aka yi masa magana a kan abin da ya hana shugaban Najeriya karbar madadin takardar shaidar karatunsa, jami’in ya ce ba su buga sabon satifiket. 
"Ba mu dauke da satifiket din da aka gabatarwa hukumar INEC a hannunmu domin ya riga ya karbe shi."