Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya aminta da ganin watan Shawwal a yau Assabar 29 ga watan Ramadan 1446 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris 2025.
Sarkin Musulmi ya ce a bayanan da suka samu na ganin wata a wurare daban daban a Nijeriya ga shugabanni kamar Shehun Borno da Sarkin Zazzau da Sarkin Kabin Argungu da Sarkin Maru da jagororin IZALA mai hidikwata a Jos da sauran mutane don haka Azumin watan Ramadan ya zo karshe daga yau Assabar gobe Lahadi ne daya ga watan Shawwal.
Allah ya karbi ibadarmu a yi wa kasa addu’a.





