Kwankwaso ya tabbatar da batun haɗewa da Peter Obi

Kwankwaso ya tabbatar da batun haɗewa da Peter Obi

Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, a yau Asabar, ya ce jam’iyyarsa na tattaunawa da jam’iyyar Labour Party da kuma ɗan takararta na shugabancin ƙasa, Peter Obi, kan yiwuwar kafa kawancen hadin gwiwa a babban zaɓen baɗi.

“Gaskiya muna tattaunawa da Peter Obi kuma an kafa wani kwamiti da ya ke aiki don duba yadda za a yi ƙawancen a tsakaninmu.

"Tabbas ƴan uwa da abokan arziki na ta zarya domin tattaunawa kan shirin haɗewar,” in ji Kwankwaso.

"ƙawancen na da muhimmanci domin kamar yadda ku ke gani jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP ba su zabi ‘yan takarar su daga yankin Kudu maso Gabas ba", inji Kwankwaso.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa  NNPP ta Kwankwaso tana da ɗumbin magoya baya a Arewacin kasar nan, musamman yankin Arewa maso Yamma,  yayin da shi kuma Obi ya fice daga PDP kwanan nan ya koma jam’iyyar Labour Party kuma yana da ɗumbin magoya baya matasa a kudancin kasar nan.

Sai dai kuma, a bisa ka'ida ba abu ne mai yuwuwa hadakar tsakanin bangarorin biyu ba kafin babban zaben shekara mai zuwa.

Abin da zai yiwu shi ne kawancen da zai iya ganin magoya bayan ko wacce jam'iyya za su zabi 'yan takarar a yankunan da suke da karfi.