Kwamishinan Ruwa Ya Kalubalanci Naseer Bazzah Kan Matsalar Karancin Ruwa a Birnin Sakkwato

Kwamishinan Ruwa Ya Kalubalanci Naseer Bazzah Kan Matsalar Karancin Ruwa a Birnin Sakkwato

 

Kwamishinan Ruwa a jihar Sakkwato Dahiru Yusuf Yabo  ya kalubalanci mataimakin shugaban matasan jam'iyar APC Naseer Bazzah kan maganarsa ta matsalar karancin ruwa a birnin Sakkwato.

Kwamishinan a wani rubutu da ya wallafa a turakarsa ta Facebook ya nemi Bazzah da ya cigaba da rubutu kan matsalar ko ya bari ruwansa, abin da ke nuni da kalubalantarsa ne ya yi don haka ya yi nazari kan abin da zai fitar da shi.   
"Ka nemi izni wajen ubangidan ku Aliyu Magatakarda Wamakko kami ka yi magana ko rubutu game da matsalar ruwan Sha a cikin Sokoto. Saboda yaro kake, amma in kana yi ne da umurni ko izni sa to kar ka fasa ka cigaba!", Kalaman Kwamishina kenan.
A wani rubutu na mayar da martani Bazzah ya nuna kwamishina ya mayar da hankali ga abin da ba shi da muhimmanci kan abin da ya bijiro da shi na matsalar ruwan sha a Sakkwato.
Ya ce tun da Gwamna Tambuwal baya kasa kamata ya yi kwamishinan ya yi bayani kan dalilan da suka sanya samun matsalar karancin ruwa a jiha, ba mayar da hankali kan Wamakko ba.
Birnin jihar Sakkwato na fuskantar matsalar karancin ruwa sosai abin da ya dauki tsawon lokaci ana fama da shi, ba tare da shawo matsalar ba.