Kuskuren Da Ke Cikin Ware Biliyan 3.7 Don Sayawa Sakkwatawa Abinci Da Gwamnati Za Ta Yi

Kuskuren Da Ke Cikin Ware Biliyan 3.7 Don Sayawa Sakkwatawa Abinci Da Gwamnati Za Ta Yi
 

Gwamnatin jihar Sokoto ta ware kudi kimanin naira biliyan 4 don siyan kayan abinci da za a raba a fadin kananan hukumomin jihar 23. 

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, wannan na daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi don ragewa al'ummar jihar radadin cire tallafin man fetur. 
Da yake jawabi ga manema labarai a zauren fadar gwamnati  bayan taron majalisar zartarwa na jihar a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, kwamishinan harkokin addini, Sheikh Dr Jabir Maihula, ya ce gwamnan jihar, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da siyan kayayyaki don rabawa. 
"Mambobin majalisar zartarwa na jihar a taronsu sun amince da siyan buhuhunan shinkafa yan 50kg guda 57,000 kan kudi naira biliyan 2.508. 
"Majalisar ta kuma amince da siyan wasu buhuhunan gero yan 100kg guda 26,000 kan kudi naira biliyan 1.430." 
Ya ce kayayyakin sun hada da buhuhunan masara 44,000 wanda gwamnatin tarayya za ta siya da hadin gwiwar gwamnatin tarayya, rahoton Nigerian Tribune. 
Ya yi bayanin cewa gwamnan ya kafa wani kwamitin da zai kula da rabon kayan abinci a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.
Kuskuren da ke cikin ware kudin don a saye kayan abinci bai wuce a ba da abincin kyauta ba, domin tsarin kyuata ba abu ba ne da zai dore ba, kuma a kullum mutane na bukatar abinci da gwamnati ta yi tsari sayar da abincin ga mutane a rahusa da abu ne da ke iya daurewa har a fita cikin wannan matsin da ake ciki. 
A misali buhun shinkafa da za a saya kwano miliyan daya ne za a samu ta yaya za a raba abincin a jihar da ke da mutane miliya 6, in har za a baiwa mutane miliyan daya kenan kowane mutum zai samu kwano daya ne na shinkafa ta yaya ka rage masa radadi a haka? Akwai bukatar gwamnati ta sauya tunani in dai tana nufin samar da sauki ga mutanenta.
A halin da ake ciki, domin saukakawa mutane zirga-zirgan ababen hawa, majalisar dokokin jihar ta kuma amince da siyan motoci masu zaman mutum 18 guda 50, samfurin 2022 a kan naira biliyan 2.8.
Ta kuma ware sama da miliyan 560 don siyan motocin Toyota Camry sumfurin 2022 guda 20, domin jigilar mata a jihar. 
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa za a hada motocin da wasu bas 10 da rukunin kamfanin BUA ya bayar tallafi a kwanan nan.