Kungiyoyin Kwadago Na  NLC Da TUC Sun Janye Yajin Aiki

Kungiyoyin Kwadago Na  NLC Da TUC Sun Janye Yajin Aiki

Kungiyoyin ƙwadago, NLC da TUC sun janye yajin aikin da suka fara yi jiya a fadin Nijeriya.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ƙungiyoyin ƙwadagon sun shiga ganin aikin ne sakamakon abinda suka kira da cin zarafin shugaban su na ƙasa, Joe Ajaero a Jihar Imo.

Sai dai kuma a daren nan ne kungiyoyin ƙwadagon suka samar da janye yajin aikin.

Hakan dai ba ya rasa nasaba da shiga tsakani da Mai baiwa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya yi a yau Laraba.

Tuni ma kungiyar ta sanar cewa ta janye yakin aikin jim kaɗan bayan ganawa da Ribadu.