Kungiyar Zakka da Wakafi ta mata ta raba Zakka a Sakkwato
Mace 30 ne suka amfana da zakkar wannan shekara a Sakkwato—shugabar kungiyar zakka da wakafi na mata
Shugabar Kungiyar Zakkah da Wakafi ta mata Malama Amina Sakaba ta shawarci matan da suka amfana da zakkar wannan shekara da kungiyarsu ta raba da su yi amfani da ita ta hanyar da ta dace domin dogaro da kai.
Shugaba Amina a wurin rabon zakkar kudi dubu 600 da aka baiwa mace 30 kowacensu ta amfana da dubu 20 ta shawarci matan da su yi amfani da kudin ta hanya hudu.
"A duk sanda mutum ya samu kudi kar ya wuce wadannan abubuwan, ya biya bashi, yayi jari(sana'a), ya saye abinci, ya yi sadaka, hakan kawai zai sa ya amfani kansa da dukiyar da ya samu," in ji Sakaba.
Malam Lawal Maidoki shugaban hukumar Zakkah da wakafi ta jihar Sakkwato ya yabawa kungiyar kan fitowa da irin wannan tunani a samu kungiyar mata dake karbar Zakkah da wakafi abin a yaba ne domin addini tafiyaar da shi yana kan mata da maza.
Ya kuma kalubalance su da a samar da wata rana ta baje kolin aiyukkan alheri a tsakanin kungiyoyi domin ankarar da sauran mutane ga aikata alheri.
managarciya