Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Kebbi Da  Gwamnonin Jihohi 4

Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Kebbi Da  Gwamnonin Jihohi 4


Kotun kolin kasar nan ta sanya ranar Juma’a 19 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan takaddamar zaben gwamnan da ya gabata a jihohi biyar. 
Jihohin da kotun zata yanke hukunci kan kararrakinsu idan Allah ya kaimu gobe Jumu'a sun haɗa da Ogun, Kebbi, Nasarawa, Gombe da kuma Delta, kamar yadda The Nation ta rahoto. 
Hakan na kunshe ne a tsare-tsaren ayyukan da kotun zata yi wanda ya fito yau Alhamis, 18 ga watan Janairu, 2024. 
Kotun za ta yanke hukunci kan kararraki biyu da suka shafi Ogun, masu lamba SC/CV/1221/2023 na Oladipupo Adebutu, ɗan takarar PDP da SC/CV/1223/2023 da Gwamna Abiodun na APC ya shigar. 
A ƙarar da suka ɗaukaka zuwa gaban kotun ƙoli, Adebutu da PDP sun nemi a soke nasarar Abiodun. 
A bangaren Gombe, kotun na shirin yanke hukunci kan karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Jibrin Barde, ya shigar yana neman tsige Inuwa Yahaya na APC. 
A shari'ar Delta, kotun na shirin yanke hukunci kan kararraki uku, wanda dan takarar jam’iyyar APC, Ovie Omo-Agege ya shigar. Dan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Kenneth Gbagi da kuma Kennedy Pela na Labour Party ne suka shigar da ragowar ƙararrakin biyu. 
 Shari'ar zaben Gombe A bangaren Gombe, kotun na shirin yanke hukunci kan karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Jibrin Barde, ya shigar yana neman tsige Inuwa Yahaya na APC. 
Dangane da Nasarawa, kotun kolin za ta yanke hukunci kan kararraki hudu da dan takarar jam'iyyar PDP, Emmanuel David Ombugadu ya shigar. 
A batun Kebbi kuma kotun mai daraja ta ɗaya zata yanke hukunci kan ƙararraki uku. Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Aminu Bande ne ya shigar da guda ɗaya. Gwamna mai ci, Nasir Idris na APC ya shigar da ƙara ɗaya yayin da mataimakin gwamna, Abubakar Umar Argungu, ya miƙa ragowar ta ukun.