Kotu Ta Yankewa Shaikh AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa

Kotu Ta Yankewa Shaikh AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa

Mai shari'a Sarki Yola a kotun shari'ar musulunci dake Kano ya tabbatar da duk maganganun da Abduljabbar yake yi shi ya kirkira kuma ya jinginawa ma'aiki.
Mai shari'a ya tabbatar da cewa maganganun fassara hadisan manzon Allah da Abduljabbar yace kage ne ko jingina ne, karya yake kuma hasali ma shine ya jingina kalmomin ga Ma'aiki. 
A cewar Alkali sashi na ɗati uku da sittin da uku sashin (f) ya bada hukunci haka:
Anyekewa Abduljabar hukuncin kisa Ta hanyar rataya Saahi 380 ne ya bada wannan hukuncin ta hanyar rataya.
Kuma kotu ta kwace litttafansa da ya gabatar da su a gaban kotu dan sheda Kuma kotu ta bada umarnin kwace masallatansa gudu biyu Na filin Mushe dana Unguwar sabuwar Gwandu.