Home Siyasa Kotu ta soke zaɓen fidda gwani na sanata a Zamfara, ...

Kotu ta soke zaɓen fidda gwani na sanata a Zamfara, ta ba da sati biyu a sake sabon zaɓe

104
0

Daga Aminu Abdullahi Gusau

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gusau ranar Litinin ta soke zaɓen fidda gwani da INEC da Jam’iyyar APC suka gudanar a mazabar Sanata ta Zamfara ta arewa.

Alkali mai kula da shari’a, Mai Shari’a Hassan Dikko ne ya sanar da soke zaben, yayin da ya yanke hukunci bayan kimanin sa’o’i biyu na zaman sauraren ƙara, inda ya yi la’akari da jawabai da hujjojin da masu ƙara da waɗanda ake ƙara suka amince da su.

Mai shari’a Dikko ya yanke hukuncin cewa a gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na APC a mazabar Sanata cikin kwanaki 14.

Idan baku mantaba, a lokacin zaɓen fidda gwani na APC da aka kammala kwanakin baya, anyi amfani da sulhu tsakanin Yan takara inda ita jam’iyyar APC da hukumar zabe ta kasa sunka aminta dayin sulhun,hakan yasa jam’iyyar ta yi la’akari da shi gaba ɗaya inda ake ɗaukar dukkan ‘yan majalisa a matsayin ‘yan takara kai tsaye.

Amma shari’ar da aka yi a mazabar Sanata ta Arewa ta Zamfara ta bambanta, kasancewar Sanatan da ke kan mulki a yanzu, Sahabi Ya’u ya kasance a kan kujerar na tsawon wa’adi biyu ba tare da kawo ma yankin nasa romon dimokutadiyya ba, babu wani ci gaba a wannan mazabar tasa.

Sahabi Ya’u shi ma ɗan yankin Kaura ne wanda ya mamaye kujerar Sanata tun daga ƙirƙirar jihar Zamfara har zuwa yau ba tare da barin wata dama ga yan siyasar yankin dasu nemi wannan kujerar ba.

Da yake jawabi ga magoya bayan sa Jim kadan bayan samun nasaran soke zaben fidda gwani wadda ya kalubalanta, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC a matakin kasa da jiha da su yi la’akari da takararsa tare da bai wa mutanen Shinkafi damar wakiltar gundumar dattawa a wannan lokacin dimokuradiyya.

A matsayinsa na dan kasa mai bin doka, Sani Abdullahi Shinkafi ya nemi hakkinsa a kotu bayan bin tsarin shari’a, kuma yanzu, kotun ta yanke hukunci a kan hanya madaidaiciya.

APC da INEC ya kamata su bar Sahabi Ya’u Kaura da Sani Abdullahi Shinkafi su tsaya takara a mazabarsu su kuma ba wa jama’a da wakilan gundumar mazabar Zamfara ta Arewa damar kada kuri’arsu.

A martaninsa ga hukuncin, dan takarar Sanata na APC, Dr Sani Abdullahi Shinkafi, ya nuna godiyarsa ga hukuncin kotun, yana mai cewa ya dawo da kwarin gwiwar mutane ga bangaren shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here