Babbar Kotun jiha ta 4 a Gombe karkashin Mai shari’a Joseph Ahmed Awak, ta yankewa wani Uba mai suna Haruna Musa da abokinsa Yakubu Abubakar da suke zaune a Unguwar Baganje dake karamar hukumar Kaltungo hukunci daurin 22 a gidan Yari bisa hadin baki da yin lalata da ‘ya’yansa biyu.
Kotun ta samu mutanen biyu da laifin hadin baki da kuma aikata fyade kan yaran biyu kananan masu shekaru 9 da kuma shekara 7.
A cikin watan oktoban shekarar ta 2019 ne mutanen biyu waton Haruna Musa yake lalata da 'yarsa kuma sai ya tura dayar gidan abokinsa Yakubu Abubakar shi ma yake lalata da ita, in da suke musu barazanar duka na cewa kar su fadawa kowa.
Kotun ta tabbatar aikata hakan laifi ne a dokar kasa sashi na 97 da sashi na 282 na kundin laifuka da hukunci na doka.
Lauyar gwamnati ita ce mai gabatar da karar Barista Hafsat Aliyu Abubakar, ta gabatar da shaidun ta na mutum 6 a gaban kotu kuma suka tabbatar da faruwar lamarin, anan ne lauyyan wadanda ake tuhuma ya yi musu wasu tambayoyi.
Lauyan wadanda ake tuhuma Barista Yakubu Chidima, ya gabatar da nasu shaidun na mutum biyu wato kannen wadanda ake tuhuma, inda ita ma lauyar gwamnatin ta yi musu wasu tambayoyi, sai dai wadanda ake zargi sun gaza kare kan su.
Mai Shari’a Joseph Ahmed Awak, ya yanke musu hukuncin zaman gidan gyaran hali, Mahaifin yaran biyu daurin shekaru 17, a ya yin da shi kuma abokin nasa aka yanke masa hukuncin shekaru 10.