Kotu Ta Baiwa Tinubu Wa'adi Don  Kawo Karshen Matsalar Tsadar Rayuwa a Najeriya

Kotu Ta Baiwa Tinubu Wa'adi Don  Kawo Karshen Matsalar Tsadar Rayuwa a Najeriya

 

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Ikoyi, Legas ta umurci gwamnatin tarayya da ta kayyade farashin kayayyaki da man fetur cikin kwanaki bakwai. Mai shari’a Ambose Lewis-Allagoa ne ya bayar da umarnin a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, a wata kara da 'dan rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN ya shigar, rahoton The Nation. 

"Wannan hukunci ne kan karar da Femi Falana ya shigar mai lamba FHC/CS/869/2023, inda ake ake karar, antoni janar na tarayya da hukumar kula da farashi ta kasa. "Kotu ta gano cewa wadanda ake karar ba su mayar da martani kan wannan karar ba duk da cewa an aika masu da takardar karar." 
"Don haka ne wannan kotun, ta karbi dukkanin rokon da mai shigar da karar ya gabatar gaban kotun. "Kotu na umurtar gwamnatin Najeriya ta kayyade farashin madara, fulawa, sukari, gishiri, kekuna, ashana, babura, motoci da kayayyakin gyaransu." Alkalin ya umurci gwamnatin Najeriya da ta sanya farashin madara, garin pilawa, gishiri, sikari, keke, ashana, babur, mota da kayan fetur da suka hada da dizal, man fetur da kananzir.