Kotu Ta Baiwa PDP Damar Gudanar Da Taronta Kamar Yadda Ta Shata
Uche Secondus na adawa da babban taron jam'iyyar PDP din ne a cewarsa bai kammala wa'adinsa ba na shugaban Jam'iyyar PDP. Sai dai kotun tayi fatali da karar da ya shigar a gabanta, inda ta baiwa Jam'iyyar damar cigaba da shirye shiryen babban taronta na kasa da za ai a babban birnin tarayya Abuja a ranakun Asabar da Lahadi. Da yawan mutane ba su yi tsammanin ya samu nasara ba domin cire shi da uwar jam'iya ta yi yana kan dokar jam'iyar.
PDP zata gudanar da babban taronta kamar yadda ta tsara 30-31 ga wannan watan na Oktoba Assabar da Lahadi kenan.
Kotu tayi watsi da bukatar tsohon shugaban Uche Secondus na hana babban taron PDP na kasa
Babbar kotun tarayya dake birnin Fatakwal ta yi watsi da bukatar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP Uche Secondus ya gabatar gabanta yana mai rokon ta dakatar da babban taron jam'iyyar da za a yi a karshen makon nan domin zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.
Uche Secondus na adawa da babban taron jam'iyyar PDP din ne a cewarsa bai kammala wa'adinsa ba na shugaban Jam'iyyar PDP. Sai dai kotun tayi fatali da karar da ya shigar a gabanta, inda ta baiwa Jam'iyyar damar cigaba da shirye shiryen babban taronta na kasa da za ai a babban birnin tarayya Abuja a ranakun Asabar da Lahadi.
Da yawan mutane ba su yi tsammanin ya samu nasara ba domin cire shi da uwar jam'iya ta yi yana kan dokar jam'iyar.
Secodus da yawan masu goya masa baya sun shawarce shi da kada ya je kotu amma ya yi ƙememe ya tafi, sai bayan kammala shari'ar ne za a ga gaskiyar lamari.
managarciya