Ko Tambuwal Yasan Lamiɗo Ya Yi Waɗannan Ga Mutanen Sakkwato Ta Gabas

A gefen Karatunsu ya ɗauki nauyin karatun Marayu kusan 100 a makaratu daban-daban, akwai marayu 5 dake karatu a Abuja mata uku, maza biyu, sai 15 da ke karatu a Teemah Academy, 10 Alhuda, 10 a C. O. E, 20 a Poly, jami'ar Ɗanfodiyo akwai 5, dukkansu a jihar Sakkwato. 

Ko Tambuwal Yasan Lamiɗo Ya Yi Waɗannan Ga Mutanen Sakkwato Ta Gabas
Gov. Tambuwal and Ibrahim Lamido

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a wani bayani da ya yiwa magoya bayan jam'iyar PDP a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyar, ya nuna shugabannin jam'iyar APC a jihar Sakkwato ba su yi wani abin a zo a gani ba a harkar tsaro duk da suna rike da manyan mukamai a bangaren tsaron.

Tambuwal ya ƙalubalanci cewa ba a yi komai ba ga sha’anin tsaro ‘ko jaje ba a je aka yi ba, dukkan manyansu ba su je jaje a gabascin Sakkwato, ba za mu yarda a gurɓuta zaman lafiyar da muke da shi ba'.

Kan wannan  muke ganin matuƙar dacewa a sanar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da mutanen Sakkwato ƙoƙarin da Dan Takarar Sanata a yankin Sakkwato ta Gabas cikin jam'iyar  APC Alhaji Ibrahim Lamido ya yi wa mutanen Sakkwato ta Gabas duk da shi don Allah ya yi, amma ya zama wajibi mu sanar.

Matsalar tsaro a yankin Sakkwato ta Gabas ta sanya wasu mutane zama 'yan gudun hijira, wasu sun zama marayu, wasu sun zama zawarawa, wasu sun rasa lafiyarsu, su ne manyan matsalolin da mutane suka ci karo da su yankin.

'Yan Gudun Hijira

Ibrahim Lamido tun sanda matsalar tsaro ta fara a  yankin ya samar da abinci daga kan Gero da Dawa da Masara da Garin-kwaki  aka riƙa baiwa mutanen yankin da suke gudun hijira a Sakkwato da ƙasar Nijar da cikin garin Sabon Birni da Isa da sauran wurare, domin ganin sun rage raɗaɗin wahala ta rasa mahallansu. Ya kuma raba barguna na rufa gare su domin maganin sanyi da tabarmi da butoci. Yakan ba da wannan gudunmuwa ne lokaci-lokaci domin sauƙaƙa wahala ga mutanen, har yanzu da kake karanta wannan rubutun bai gaji ba.

Marayu

Su ne Lamiɗo ya fi tausayawa saman kowa duk tunaninsa ya ƙare kan Marayu su samu gata, ni dai abin da na sani akwai sama da gidaje 20 da yake kula da su a birnin Sakkwato da suka rasa ransu kan matsalar nan, akwai guda bawai a Isa, da wasu 10 da abinci yake kai musu da suka haɗa da dawa da gero da masara a fahimtar da yake da ita kan gidajen tallafi ne buƙatatsu ba  ɗaukar komai nasu ba.

A gefen Karatunsu ya ɗauki nauyin karatun Marayu kusan 100 a makaratu daban-daban, akwai marayu 5 dake karatu a Abuja mata uku, maza biyu, sai 15 da ke karatu a Teemah Academy, 10 Alhuda, 10 a C. O. E, 20 a Poly, jami'ar Ɗanfodiyo akwai 5, dukkansu a jihar Sakkwato. 

Zawarawa

Wasu mutane ne  abin tausayi dake buƙatar kulawa don kare mutuncinsu, Lamiɗo kamar yadda yake yiwa marayu haka bai bambanta da su ba, yakan kula da su kan abin da ya shafi abinci da kula da yaran da mijinsu ya mutu ya bar musu da samar da jari gare su tare da kula da yanayi da tsarin abin da matan ke buƙata.

Marasa Lafiya

Ibrahim Lamiɗo akwai likitoci da jami'an kiyon lafiya 'yan asalin yankin Sakkwato ta Gabas da ya ɗaurawa alhakin duk wani mutum mace ko namiji da ya samu rauni kan matsalar tsaro ko rashin lafiya ta yau da kullum, da su ɗauke shi zuwa asibiti a ƙaramar hukuma ko birnin jiha ya danganta da ciwon.

Mutanen jihar Sakkwato a asibitin Ƙwararri ta jiha da ta koyarwa ta Ɗanfodiyo da ta Ƙashi dake Wamakko suna faɗin cewa Allah ya sauwaƙawa mutanen gabascin Sakkwato da suka samu rauni sanadin harbin 'yan bindiga da ya ba su Lamiɗo, domin da ba a samu tallafinsa za a iya haɗuwa da ƙaddarar da tafi wannan muni, za ka ga an kawo mutum da harsashi a jikinsa ana buƙatar kuɗi don yi masa aiki 'yan uwa na neman abin da ma za su ci, ba maganar kuɗin aiki ba, a haka za ka ga likita ya zo masu da risit Lamiɗo ya biya kuɗin aiki gaba ɗaya, mutanen da ya yiwa haka Allah ne kaɗai yasan adadinsu domin shi baya lissafi domin don Allah ya yi, amma hali ya sa dole a faɗi a yanzu.

Kai mai karatu kana ganin wanda ya yi haka ana da wurin da za a yi masa gorin JAJE, ballantana ma Lamiɗo ya tafi ya jajanyawa mutanensa a kusan dukkan hare-haren da aka samu a yankin.

A hasashe na nasarar Lamiɗo na tare da maslahar magance matsalar tsaron yankin Sakkwato ta Gabas, domin a koyaushe fatansa ya samar da  zaman lafiya da walwala a cikin al'ummarsa da jiha da kasa baki ɗaya.

Daga Muhammad Kabiru a ƙaramar hukumar Goronyo.