'Ko Shekaru 100 Aka ba Tinubu Bai San Yadda Zai Yi da Najeriya ba' 

'Ko Shekaru 100 Aka ba Tinubu Bai San Yadda Zai Yi da Najeriya ba' 


Wani lauya dan Najeriya ya koka kan yadda Bola Tinubu ke mulkar kasar ba yadda ya dace ba. 
Lauyan da ke kasar Jamus, Franklyne Ogbunwezeh ya ce Bola Tinubu bai da kwarewar iya mulkin Najeriya. 
Lauyan ya fadi haka ne yayin wata hira ta musamman wanda jaridar TheCable ta bibiya a karshen makon da ya gaba. 
Ogbunwezeh ya ce kwata-kwata Tinubu bai nemo hanyar kawo sauyi a kasar ba duba da yadda yake jagorantar ƙasar. 
Ya koka kan tsare-tsaren Tinubu musamman duba da rugujewar darajar Naira da tashin farashin kaya, Sahara Reporters ta ruwaito. 
"Tinubu ba shi da kwarewar jagorantar Najeriya, ko da kuwa za a ba shi shekaru 100 bai san ya zai yi ba." 
Ogbunwezeh ya kalubalanci Bola Tinubu ya nuna tsari daya mai kyau da ya kawo domin dakile tashin farashin kaya da daga darajar Naira. 
Lauyan ya caccaki Tinubu bayan cire tallafin mai inda ya ce bai shirya komai kafin aiwatar da hakan ba wanda ya yi sanadin jefa al'umma cikin halin matsi.