Ki fadawa Mijinki  Al'umma Na Fama Da Yunwa-- Sarkin Kano Ga Matar  Tinubu

Ki fadawa Mijinki  Al'umma Na Fama Da Yunwa-- Sarkin Kano Ga Matar  Tinubu

Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya tura Sako ga Shugaban Kasa Bola  Tinubu ta hannun Uwargidansa Sanata Oluremi Tinubu a ziyara da ta kaiwa Maimartaba Sarki a Fadarsa. 

Maimartaba sarki yace muna da hanyoyin tura sako ga Shugaban kasa da yawa Amma kasancewar ki Uwargidan sa kinfi kowa kusanci dashi. 

Al’umma suna kawo mana kukan su na tsananin rayuwa da ake ciki a Wannan lokaci, ya kamata Gwamnati ta duba hanyoyin saukakawa Al’umma. 

Mun samu kiraye kiraye daga al’umma Akan dauke wasu manyan ma’aikatu daga Birnin Abuja zuwa Lagos kamar wani bangare na CBN da FAAN, al’umma basu gamsu da Wannan yunkurin ba, ya kamata Gwamnati ta duba sosai don tabbatar da masalahar al’umma, Idan muka Gwamnati tana da hujja mai Karfi sai tayi bayani yadda al’umma zasu gamsu.

Muna fata Wannan sako zai isa ga Maigirma Shugaban kasa.  

Daga Isma'il Lamido..