Kebbi ta dauki nauyin yara 70 su yi karatun digiri  a  Saudiyya

Kebbi ta dauki nauyin yara 70 su yi karatun digiri  a  Saudiyya

 
 
Gwamnatin jihar Kebbi ta kammala shirin ta na daukar nauyin yara 70 domin tafiya karatu a kasar Saudiya domin samun takaradar digiri na farko a kwasa-kwasai daban-daban.
Wannan hobbasar ta zo ne a cikin shirin Gwamnan Kebbi na kafa mutane da ake yi karkashin maibaiwa gwamna shawara kan harkokin addinai Injiniya Imran Usman.
Ya ce kananan hukumomi 20 na jihar kowace za ta bayar da mutum uku in da karamar hukumar Birnin Kebbi za ta ba da mutum 10.
"Gwamnatin Kebbi za ta dauki nauyin tafiyar su zuwa kasar Saudiya haka ma ita za ta kula da harkokin karatun da walwalarsu daga sanda suka sauka," a cewarsa.
Injiniya Imran ya ce daliban da shekarunsu suka kai 18 ne kadai za a aminta da a tantance su don su ne za su yi cika ka'idar kasar Saudiya da aka sanya kan karatun.
"Masana daga kasar Saudiya suna cikin Birnin Kebbi yanzu haka domin tantance daliban domin su kama hanya ta tafiya," ya kara da hakan.
 Kowace karamar hukuma ana sa ran ta bayar da namiji biyu mace daya domin tafiya karatun na digirin farko.
Maibaiwa Gwamna shawara ya fadi shirin su na tura Limaman Jumu'a kasar waje don  su samu horo kan yanda ake yin huduba da karatun Hadisi don kara fadada karatunsu, su ilmantar a lokacin sallolin Jumu'a.