Kashe Sarkin Gobir: Wannnan musiba ce da ta shafi yankinmu----Sanata Ibrahim Lamiɗo 

Kashe Sarkin Gobir: Wannnan musiba ce da ta shafi yankinmu----Sanata Ibrahim Lamiɗo 

Dan majalisar dattijai Sanata Ibrahim Lamiɗo da ke wakiltar yankin  Sakkwato ta Gabas ya razana kwaran da gaske kan labarin rasuwar Sarkin Gobir Isah Muhammad Bawa wanda ya rasu a hannu 'yan bindiga.
A yau Labara aka tashi da zancen rasuwar Sarki kafin akai kuɗin fansar da aka yi matsaya za a bayar don a saki Sarkin Gobir din tare da dansa.
Sanata Lamido ya bayyana rasa Sarkin Gobir wata musiba ce da ta shafi yankinsu gaba daya, ba za su zuba ido wannan lamarin ya tafi a hakan ba.
Ya baiwa dukkan al'ummar Gobirawa a duk in da suke da su yi hakuri ina ba su tabbacin jinin Sarkin Gobir ba zai tafi a banza ba.
Sanata ya yi kira ga gwamnati jiha da kasa su sauya tsarin kawar da matsalar tsaro musamman a yankin Sakkwato ta Gabas, su rika aiki tare da 'yan majalisar tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a wuraren da suke zaune.