Kasan Abin Da Ya Faru Da Dan Takarar Sanatan APC Na Sakkwato Ta Gabas A Illela?
Daga Muhammad Nasir.
Dan takarar Sanata a jam’iyar APC a yankin Sakkwato ta Gabas Alhaji Ibrahim Lamido ya ziyarci karamar hukumar Illela domin karbar mambobin jam’iyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC su sama da 180 da yin jaje kan hare-hare ‘yan bindiga a karamar hukumar da kuma bude katafaren ofishin yekuwar neman zabensa a Illela.
Ibrahim Lamido ya samu gagarumar tarba a karamar hukumar sai ka ce ana bukin sallah ne, yanda kowane mutum ke farincikin ganin jagoransa da ya aminta da ya wakilce shi a zauren majalisar dattijan Nijeriya a 2023.
Lamido ya godewa karimcin da aka yi masa, bayan jajantawa ya kuma jinjinawa mutanen Illela yanda suka rike tafiyar APC da Sanata Wamakko gam-gam, domin samun cigaba a yankinsu.
“Matsalar tsaro da ke addabar yankinmu muna daukar matakan da suka dace kuma da ikon Allah za a samu nasara, fatar mu dai mutane su ba mu goyon baya a tafiyarmu, domin don su muke wannan; ba abin da ke gabana sama da al’umma da jiha kasa ta baki daya,” a cewar Lamido.
Ya godewa mutanen da suka sauya sheka domin sun fahimci wannan tafiya ta gaskiya ce da amana kuma APC za ta tafi da su ba wani bambanci tsakaninsu da wadan da suka tarar a APC.
Lamido da tawagarsa sun kaddamar da ofishin yekuwar zabensa tare da wasu kungiyoyi sama da 10 da suka sadaukar da kansu da yin tsayin daka sai APC ta samu nasara a karamar hukumar Illele da gagarumar rinjaye, ko ba komai dai garin na jam’iyar APC ne.
Hajiya Shamsiya Sirajo amadadin wadan da suka sauya shekar, ta godewa dan takarar sanatan kan karimci da hidimtawa jama’a da yake yi a koyaushe wanda hakan ne ya sa suka karbi tafiyar APC domin cigaban al’umma ne muradinsu.
Kodinetan Lamido a Illela yaba da tabbacin samun nasarar jam’iyar APC a dukkan matakan da za a yi zabe a 2023, domin su ba za su taba mantawa da irin karimcin da tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi masu ba.
Ya ce Sanata Wamakko ya taimakawa harkokin kasuwancinsu da sha’anin ilmin matasa da samar da aikin yi a yankin gaba daya.
managarciya