Kare Manoma Ga Harin 'Yan Bindiga, Tinubu Zai Kaddamar Da Dakaru

Kare Manoma Ga Harin 'Yan Bindiga, Tinubu Zai Kaddamar Da Dakaru
 

Majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) ta amince da rabawa manoma takin zamani a saukake tare da kuma kaddamar da dakarun gona don yaƙi da 'yan ta'adda da ke farmakar manoma.

Majalisar ta ce daukar wadannan matakan za su taimaka ainun wajen magance karancin abinci, tsadar abinci, yunwa da rage matsin tattalin arziki. 

Stanley Nkwocha, babban mai hidimtawa shugaban ƙasa Bola Tinubu ta fuskar watsa labarai, ofishin mataimakin shugaban kasa ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa. 
Nkwocha ya fitar da sanarwar ne jim kadan bayan kammala taron majalisar na 139 wanda aka yi shi ta intanet bisa jagorancin Kashim Shettima, The Cable ta ruwaito. 
A yayin taron, Shettima ya yi nuni da cewa idan har aka samar da tsari mai kyau, Najeriya za ta cimma gagarumar nasara nan kusa. Abubakar Kyari, ministan noma da samar da abinci a yayin taron, ya ce gwamnati za ta gana da kamfanonin sarrafa taki irinsu Indorama, Dangote da Notore.