Karancin Naira: Jihar Zamfara Da Wasu 2 Sun Maka Buhari Kotu

Karancin Naira: Jihar Zamfara Da Wasu 2 Sun Maka Buhari Kotu

Wasu jihohin Arewa uku sun juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya kan manufarsa na sauya takardun naira inda suka maka shi a kotun koli. 

Channels TV ta rahoto cewa jihohin na Arewa da suka hada da Kaduna, Kogi da Zamfara sun nuna damuwarsu kan illar da ke tattare manufar sauya kudi na babban bankin Najeriya ya jefa mutane cikin wahala da kunci  inda suka bukaci kotun kolin da ta dakatar da aiwatar da tsarin. 
A cikin karar da suka shigar ta hannun lauyansu Abdulhakeem Uthman Mustapha (SAN), jihohin sun bukaci kotun da ta dakatar da gwamnatin Buhari da  jami'anta daga aiwatar da shirin. 
Saboda haka, jihohin na Arewa  suna so kotun ta hana gwamnatin tarayya aiwatar da wa'adin na 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000  kudin kasar Nijeriya. 
Masu shigar da karar sun ce tun bayan sanar da manufar, ana fuskantar karancin sabbin kudi a Kaduna, Kogi da Zamfara, suna masu cewa al'ummar da suka shigar da tsoffin kudadensu a banki suna fuskantar matsin rayuwa a duba lamarin.
An kuma bayyana cewa yawansu sun rasa hanyar samun sabbin kudi don gudanar da harkokinsu na yau da kullum, rahoton The Cable.