Kamfanin Siminti Na BUA Ya Kashewa Al'ummar Da Ke Zagaye Da Shi Miliyan 62 A Sakkwato

Kamfanin Siminti Na BUA Ya Kashewa Al'ummar Da Ke Zagaye Da Shi Miliyan 62 A Sakkwato

A bangaren hulda da jama'a Kamfanin siminti na BUA ya kashe kudi miliyan 62 kan samar da wutar lantarki da ruwan sha da makaranta ga al'ummar da ke zagaye da kamfanin a jihar Sakkwato.

Shugaba sashen  hulda da jama'a na kamfanin Alhaji Sada Suleiman ne ya sanar da haka a wurin bukin mika Bohol mai samar da sama da galan dubu 10 a rana da aka gina a kauyen Gidan Gamba na karamar hukumar Wamakko a Sakkwato.
Sada ya gabatar da Bohol ga shugaban karamar hukumar Wamakko Bello Haliru Guiwa ya ce sun gina asibiti da samar da na'urar wuta mai karfin makamashi 500 da 300 domin tallafawa asibitin kwararru ta Sakkwato.
Shugaban karamar hukkumar Bello Guiwa da hakimin Gidan Gamba sun nuna farincikinsu ga kamfanin BUA kan fahimta da suke da ita da kokarin taimakawa cigaban kauyukkansu.
Ya ce kamfanin BUA yana kokari ga al'ummar Wamakko ya gina makaranta ta zamani ya kuma samar da Bohol a kauyen Girabshi bayan na Gidan Gamba, ba abin da zamu ce masa sai godiya.