Home Labarai Kalaman Gwamnan Nasarawa cewa ‘bai ga ɗan bindiga a hanyar Sokoto ba’...

Kalaman Gwamnan Nasarawa cewa ‘bai ga ɗan bindiga a hanyar Sokoto ba’ sun bar baya da ƙura

19
0

Ɗan takarar gwamnan jihar Sakkwato a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Manir Muhammad Dan’iya, ya nuna matuƙar damuwarsa kan abin da ya kira yunƙurin jam’iyyar APC na raina ƙalubalen tsaron da ke addabar al’ummomin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan yaɗa labarai ga ɗan takarar, Aminu Abdullahi, ya fitar, inda Dan’iya ke mayar da martani kan kalaman Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, yayin ziyarar da ya kai garin Silame, wanda aka ruwaito ya ce jihar ba ta da matsalar tsaro bayan shi da kansa ya tuƙa mota daga birnin Sakkwato zuwa garin ba tare da ya gamu da ‘yan bindiga ba.

Dan’iya ya bayyana cewa tafiya a hanya ɗaya lafiya ba zai goge kwarewar dubban mutanen da suka fuskanci kisa, garkuwa da mutane, raba su da muhallansu, satar shanu, da karɓar haraji ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here