Home Labarai Kakakin Majalisar Dokokin  Kebbi Ya Rasu da shekara 56

Kakakin Majalisar Dokokin  Kebbi Ya Rasu da shekara 56

22
0

Rahotanni daga Jihar Kebbi sun tabbatar da rasuwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar,  Honarabul  Muhammad Usman Akwai(Lifiddan Zuru).

Marigayin shi ne mai wakiltar mazaɓar Zuru a majalisar dokokin jihar, ana sa ran za a sanar da cikakkun bayanai kan jana’izarsa nan gaba bayan an dawo da gawarsa Nijeriya daga Masar.

Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya samu labarin rasuwar shugaban majalisar in da ya bayyana rashin abin damuwa ne da bakin ciki ga mutanen Kebbi da kasa baki daya.

Margayin ya rasu ne a ranar Litinin 6 ga watan Afirilu 2026 a wata asibiti dake Cairo a Egypt, in da ya yi doguwar jinya, Kilak na majalisar dokokin Alhaji Suleiman Shamaki ya tabbatar da rasuwar.

Margaryin an haife shi 5 ga Afirilu 1970 ya bar matar Aure ɗaya da ‘ya’ya biyar a Duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here