Managarciya

Kada Ku Kuskura Ku Zabi Shugabannin da Ba Su Cancanta Ba—Sarki Sanusi


Sarkin Kano na 14, kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya ba ‘yan Najeriya shawarin irin shugabannin da ya kamata su zaba a zaben 2023 mai zuwa. 

Muhammadu Sanusi II, ya ce ya kamata ‘yan Najeriya natsu su zabi shugabannin da ke da kwarewa ta gudanar da kasa a zabe mai zuwa, kuma su kauda batun kabilanci, TheCable ta ruwaito.
Sanusi ya bayyana hakan ne a jiya Laraba 24 ga watan Agusta a jihar Legas taron The August Event 2022 da gidauniyar Moses Adekoyejo Majekodunmi tare da hadin gwiwar Asibitocin Santa Nicholas suka shirya. 
“Ya kamata a titsiye ‘yan siyasa domin su fadi shirinsu kan asibitoci da ilimi da sauran muhimman bangarorin da suke da koma baya a kasar nan. 
“Gwamnati dai ta daina mutunta wannan sana’ar kuma babu adadin kudaden da za a kashe a fannin ilimi ta albashi a kasar nan da zai kawo sauyi. 
Likitoci da malamai ya kamata gansu cikin rayuwa mai kyau da mutuntawa.
” Ya kuma bayyana cewa, bangare mafi kyau da zai gyara kowace kasa a duniya shi ne ilimi, inda ya koka da cewa, akwai bukatar martaba ilimi da kiwon lafiya a Najeriya. 
Exit mobile version