Home Siyasa 2027: APC ta musanta zargin shirin kashe Atiku

2027: APC ta musanta zargin shirin kashe Atiku

6
0

Jam’iyyar APC ta musanta zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na shirin kashe tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Alake ya mayar da martani ne kan zargin da Timi Frank, ɗan jam’iyyar ADC, ya yi cewa gwamnati na shirin kashe Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Ya buƙaci jami’an tsaro su gayyaci Frank domin ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zargin nasa.

Ya kuma musanta cewa an janye jami’an tsaron da ke gadin Atiku, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar na samun kariya daga ’yan sanda da Hukumar DSS.

A cewarsa, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaurara tsaro ga ’yan takarar shugaban ƙasa, mataimakansu da ’yan takarar gwamna a faɗin ƙasar gabanin zaɓen 2027.

Alake ya zargi wasu ’yan adawa da yin kalaman da za su iya tayar da hankalin jama’a domin neman ribar siyasa.

Ya yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu su riƙa yin kalamai masu inganci da alhaki, tare da mayar da hankali kan matsalolin da ke addabar ’yan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here