Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato 

Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato 
Jirgin ruwa ya nutse da Mutane sama da 30  da babura takwas a garin Kojiyo  cikin karamar hukumar Goronyo  a Sakkwato.
Nasiru Goronyo ya shaidawa Aminiya cewa jirgin ruwan ya yi hatsari ne a gulbin garin bayan ya dauko mutanen da kayansu domin ya ke tarar da su amma wannan lamarin ya cika da su.
"A yanzu mutane 30 da jirgin ya dauko ba wanda aka fitar da shi a ruwan, sai dai an samu fitar da babur daya daga cikin takwas da suka nutse bayan shi duk kayan mutanen da suke tare da shi ba wanda aka samu."
Abubakar Abdullahi Ghani jami'in hulda da jama'a na hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha SEMA ya ba da tabbacin faruwar lamarin, ya ce mutanen da ake zaton sun shiga jirgin 45, mutum biyar suka tsira domin sun iya ruwa, zuwa yanzu an dauko gawar mutum 10, hukumar na cigaba da kokarin fitar da wadanda suka nutse.
Ya ce a lokacin da suka samu bayanin faruwar lamarin jami'an su ba su yi kasa a guiwa ba, sun garzaya wurin har aka samu nasarar da aka fada a farko, kuma  za su cigaba da aikin ceton har fito da sauran mutanen da suka mutane.