Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn domin inganta kiwon lafiya

Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn domin inganta kiwon lafiya
Bankin Raya Ci-gaban Afirka (AfDB) ya amince da ba wa Gwamnatin Jihar Sakkwato bashin Naira biliyan 70.4 domin inganta fannin kiwon lafiya.

Wannan shiri na da nufin bunƙasa fannin kiwon lafiya da ingancinsa, da kuma cike giɓin da ake da shi a ɓangaren a Jihar Sakkwato, a cewar AfDB ta bayyana a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.

Rahotanni na nuni da cewa, yaro ɗaya cikin kowane yara 20 ne akale yi wa allurar rigakafi cikakke a Jihar Sakkwato a, a yayin da adadin mutuwar jarirai ya kai 104 daga cikin 1,000 a Jihar.

Ƙasa da kashi 14 cikin 100 na cibiyoyin lafiya a jihar ne suke da kayan aiki masu aiki, kuma likita ɗaya ne kawai ke kula da mutum 8,285, wanda ya gaza abin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar na likita 1 ga 1,000 mutum

Kuɗaɗen da bankin ya ware za su tallafa wa samar kayan aikin kula da lafiya masu inganci a matakai uku na kula da lafiya a Jihar Sakkwato.

Wannan ya haɗa da gina sabon asibitin koyarwa mai gado 1,000, da manyan asibitoci na yankuna uku masu jimillar gadaje 450, da kuma cibiyoyin kiwon lafiya guda shida da aka tsara a domin kuka da al’ummomin karkara.

Aikin ya kuma haɗa da gyaran cibiyoyin horar da ma’aikatan lafiya da ƙirƙirar sabon ma’ajiyar magunguna ta zamani.

Darakta-Janar na Ofishin AfDB a Najeriya, Abdul Kamara, ya ce, “Wannan rancen na nuna yadda muke jajircewa wajen aiki tare da gwamnati don magance giɓin kayan kiwon lafiya a Najeriya, tare da gina cibiyoyin kula da lafiya masu ƙarfi da suka dace da tsari na yanayi.

“Ta hanyar ƙarfafa kayan aikin lafiya a Jihar Sakkwato, muna gina fata da hanyoyin samun kyakkyawan sakamako ga miliyoyin ’yan Najeriya.”