Jihar Rivers: Fubara ya bada kai bori ya hau  ya gayyaci ƴan majalisar da ke goyon bayan Wike

Jihar Rivers: Fubara ya bada kai bori ya hau  ya gayyaci ƴan majalisar da ke goyon bayan Wike

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gayyaci Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Martin Amaewhule, da sauran ‘yan majalisa zuwa wani taro.

An shirya taron ne  a Ofishin Gwamna, da ke Fadar Gwamnati a Fatakwal, ranar Litinin.

Wannan sanarwa ta fito ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 7 ga Maris, wacce gidan Talabijin na Channels  ta samu a ranar Lahadi.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Tammy Danagogo, ne ya sanya hannu kan wasikar.

"Wannan wasika tana zuwa ne a ci gaba da alkawarin da Mai Girma Gwamna ya yi a wasikata mai kwanan wata 5 ga Maris, 2025, don sanar da ku cewa Mai Girma Gwamna ya karɓi hukuncin Kotun Koli, don haka ya umarce ni da in gayyace ku da sauran ‘yan majalisar dokokin Jihar Rivers zuwa taro," in ji wani ɓangare na wasikar.